MDD ta yi Allah-wadai da hare-haren Isra’ila a kan fararen hula
Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi Allah-wadai da hare-haren Isra’ila da suka yi sanadiyar illata dubban fararen hula a arewacin Gaza.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dubban mutane na cikin tsananin rashin abinci da sauran kayan buƙatun yau da kullum.
Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta zargi Isra’ila da wargatsa Gaza da kuma cutar da Falasɗinawan da ba su ji ba, ba su gani ba.
Sanarwar ƙungiyar ta biyo bayan harin da Isra’ila ta kai a wajen rabon abinci a sansanin ƴan gudun hijirah na Jabalia da ke arewacin Gaza lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 10.