Gwamnatin jihar Neja ta dakatar da biyan albashi saboda shaidun ɗaukar aiki na boge

Gwamnatin jihar Neja ta koka kan yadda wasu da ake zargi da damfara sun kwaikwayi tamardar daukar aiki ta gwamnatin jihar tare da daukar ma’aikatan da a yanzu ke kan tsarin albashin gwamnati.

Arewa PUNCH ta samu labarin cewa ayyukan wadannan ‘yan damfara ne ya janyo tsaikon albashin watan Satumba ga wadanda ake biya na gaskiya.

A sakamakon wannan ci gaban, kwamishiniyar yada labarai da dabaru, Binta Mamman ta sanar da cewa, a yanzu ya zama tilas a tantance dukkan masu rike da mukaman siyasa a yunkurin da ake na fitar da masu almundahana a tsakanin su.

Mamman ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar inda ta maida shi wajibi ga dukkan ma’aikatan, inda ta kara da cewa wanda suka haye tantancewar ne kadai za a biya su albashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *