Ingila ta fara zawarcin Guardiola, United ba ta cire rai kan Eze ba

Ingila ta fara zawarcin Guardiola, United ba ta cire rai kan Eze ba

Ingila ta fara zawarcin Guardiola, United ba ta cire rai kan Eze ba
Ingila ta fara zawarcin Guardiola, United ba ta cire rai kan Eze ba

Hukumar Kwallon kafan Ingila ta nuna sha’awar daukar Pep Guardiola, ɗan ƙasar Sifaniyan na tunanin tsawaita kwantiraginsa da Manchester City, an shaidawa Lee Carsley cewa ba za a naɗa shi kocin Ingila na dindindin ba.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta bayyana kocin Manchester City Pep Guardiola, mai shekaru 53, a matsayin wanda ke kan gaba a jerin sunayen waɗanda ta ke nazarin ɗauka ya zama kocin Ingila, kuma ana sa ran zai yanke shawara kan makomarsa nan da makonni masu zuwa. (Times)

Guardiola kuma tauna batun rattaba hannu kan kwantiragin shekara guda domin ya ci gaba da zama a Man City(Telegraph)

Manchester United ta sa ido kan ɗan wasan Crystal Palace Eberechi Eze, mai shekara 26, inda har yanzu ba ta cire rai kan ɗan wasan na Ingila ba, bayan ta shafe kakar bara tana zawarcinsa. (Football Transfers)

An shaida wa kocin riƙon ƙwarya na Ingila Lee Carsley cewa ba zai samu aikin jan ragamar tawagar na dindindin ba. (Sun)

Liverpool na son ɗaukar ɗan wasan baya Loic Bade a matsayin wanda zai maye gurbin kyaftin ɗin Netherlands Virgil van Dijk, mai shekara 33. Sai dai Sevilla ba za ta saurari tayin ƙasa da Yuro miliyan 20 kan dan ƙasar Faransa mai shekara 24 ba. (Mundo Deportivo)

Barcelona ta nuna sha’awarta na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Arsenal da Ghana Thomas Partey, mai shekara 33. (Goal)

Tsohon dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 31, zai iya fara taka leda a watan Maris na 2025 bayan da aka rage tsayin dakatawar da aka yi masa amma da wuya ya sake bugawa Juventus wasa. (Fabrizio Romano)

Pogba ya yi watsi da tayin ƙungiyar Broke Boys FC na Rasha. (France Football)

Kamfanin wasanni na A22 yana ɗaukar matakai don ƙaddamar da gasar Super League a watan Satumba na 2025. (AS)

Newcastle United na shirin karɓar tayi kan ɗan wasan tsakiya na Paraguay Miguel Almiron, mai shekara 30, a watan Janairu a wani yunƙuri na tara kuɗi don sake sabunta tawagar ƴan wasanta. (Football Insider)

Manchster United za ta iya sake siyan ɗan wasan bayan Sifaniya Alvaro Carreras, mai shekara 21, wanda ya bar Old Trafford zuwa Benfica a bazara.(Mirror)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *