Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima,

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnatin tarayya na tausayawa ‘yan kasa, musamman ma talakawa a cikin halin kuncin rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki, inda ya bayyana cewa gwamnati ba ta da wani zabi ne na fitar da yan kasan daga halin da suke ciki a yanzu.

Shettima ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Litinin yayin bikin cika shekaru 30 da fara taron tattalin arzikin Najeriya.

Ya kare manufofin tattalin arziki na gwamnati mai ci, yayin da ya bayyana matakan da gwamnati ta dauka na inganta tattalin arzikin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *